Hook
More breakout videos from this creator.
Wannan mutumin yana da hancin mafi kaifi a duniya. Lokacin da ya dauka jarida ya dan sha ka ta kadan, nan take ya gane cewa sabuwar jarida ce da aka buga ta yanzu. Sai wani mutum mai filasta a hannu ya wuce kusa da shi. A nan mutumin ya sake jiyo wani wari mai ban mamaki. Nan take ya sanarwa ma'aikaciyar jirgin cewa akwai dan ta'adda a cikin jirgin da yake dauke da bam. Tabbas akwai dan ta'adda a cikin jirgin da yake dauke da bam. Lokacin da kaftin ya zo yana ta gazgatawa da shakka, sai ya tambaye shi ta yaya ka tabbatar da hakan? Nan mutumin ya amsa cikin natsuwa ya ji kamsin bam din. Amma kaftin din bai yarda da shi ba, amma ya dauka cewa mutumin ya haukace. Domin ya tabbatar musu yana da gaskiya, sai mutumin ya fito da wani sirrin makamin da yake da shi. Da kaftin ya gani sai ya yi mamaki sosai, kuma daga karshe dole ya yarda da mutumin. Saboda karfin jiyo kamsin sa, mutumin ya ceto rayuwar kowa da kowa da suke cikin jirgin. Amma a daidai wannan lokacin sai tsohuwar matarsa ta kira shi. Ta ce dan su an kama shi yana shan taba a makaranta, kuma dole ne ya je ya ga shugaban makarantar. Mutumin ya yi sauri ya nufi makarantar. Da ya isa shugaban makarantar ya gaya masa cewa an kama dan sa da wasu yara suna shan taba a garejin makarantar, sai ya nuna masa sigarin a matsayin shaida. Mutumin ya dauki sigarin ya dan sha ke shi kadan, sannan ya ce wannan ba kamsin dana bane. Sai ya bi sa'ar kamsin har ya kai shi dakin gwaje-gwaje na kimiyya. Daga nan sai ya tsaya kusa da wani yaro, ya dauki jaka a kasa sai ya tambayi yaron, wannan jakar taka ce? Yaron ya yi shiru bai amsa ba. Sai mutumin ya je ya fadi da kansa gefe cikin sauki, nan take tarin sigari suka fito daga cikin jakar. Cikin natsuwa ya ce wannan shi ne asalin mai supplier, ya wuce abunsa ya tafi, ya bar principal a tsaye a wurin.