Hook
More breakout videos from this creator.
Kullu amakaranta, abokan karanta abokan karatun wannan yarinyar suna cin zarafin ta. Amma bata taba yin kora ramawa ba. Abokan karatun suna dafawa ta shara har ma suna dafawa ta takalmin su. Wani babban dalibi mai kirki ya kasa cigaba da kallon abinda suke yi. Nan take ya shiga tsakani yana wannan daliban cigaba da cin zarafin ta. Bayan an gama taron safe, sai ya garzaya wurin yarinyar dan ya tambaye ta ko tana bukatar taimako. Amma a daidai wannan lokacin, yarinyar ta ji tsoro dan ya taba ta ta kwala wani ihu sosai. Kiyosumi ya tsaya cak sabida mamaki. Kamun ya samu damar bayyana kansa, sai yarinyar ta sake yin ihu. Daga nan ta gudu kamar wata ta rasa hayyacin ta. Sauran daliban suka tsaya suna kallon ta cikin shuru, kamar sun riga sun saba da irin wannan halayen ta. Ba da dadewa ba labarin abinda ya faru a taron safe ya bazu a duk makarantar gabaki daya. Sabida Kiyosumi yayi kokarin taimaka wa yarinyar, har abokan karatun sa suka bashi wani mummunan lakabi. Abokan karatun sa suka gaya masa sunan yarinyar Hari Kuramoto. Suka ce bata cika zama kamar sauran mutane ba, kuma duk wanda ya shiga harkar ta zai gamu da rashin sa'a. Kowa a ajin su ya tsane ta. Koda yake abokan karatun sa basu bayyana komai dalla dalla ba, Kiyosumi ya tabbatar da a guda daya. Wannan ba komai bane face cin zarafin da ake ma Hari. Kiyosumi mutum ne mai tsananin son adalci. Tun yana dan karami baya iya jurewa idan yaga ana zaluntar wani. Sabida haka ba tare da bata lokaci ba ya nufi ajin su Hari kai tsaye. Amma abinda ya gani a wurin ya kara tayar masa da hankali. Ya gan kowani dalibi a cikin ajin su Hari yana cin zarafin Hari. Suna cigaba da yi mata kalamai masu zafi da ban kyama. Hari tayi kama da wata yar tsana da aka tura ta cikin kusurwa. Jikin ta cike da raunin ka, ta tsaya kawai cikin rashin karfi bata iya yin komai ba. Yana tsaye a wajen kofan ajin, nan take ya yi ihu ya ce su daina. Amma da sauran ajin suka gan shi basu ji tsoron sa ba. Koda sabida shi babban dalibi ne basu ji tsoron sa ba. Maimakon hakan sai suka kara tsananin abinda suke yi. Nan Kiyosumi ya matsa gaba a gaban kowa a cikin ajin. Ya taimaka wa Hari ta daga tebura da kujerun da aka ki fado. Yana ganin cewa idan ya tsaya mata cin zarafin zai daina. Amma har yanzu bai fahimci irin muguntar da mutanen da zasu iya yi mata ba. Bayan an tashi daga makaranta, yana kan hanyar sa ta komawa gida. Sai ya ga wasu yan mata suna dafawa takalma a ko ina. Nan Kiyosumi ya dauke daya daga cikin takalman, sai ya gane cewa takalman Hari ne. Amma abinda ya faru daga baya ya fi muni. Sun kuma lalata sunan da aka rubuta a jikin akwatin takalman ta. Kiyosumi ya ga komai, ya kuma adana abinda ya gani a cikin zuciyar sa. Washe gari bayan an tashi daga makaranta, sai ya sake ganin takalman Hari a watsa a kasa. Sai ya dauke su ya mayar da su cikin akwatin takalman ta. Daga nan ya cire sabon stikan sunan ya rubuta wani sabo Hari Kuramoto a kai, sannan ya manna shi a kan wanda aka lalata. Yayi fatan hakan zai rage mata dan kunya da wahalar da take sha kullum. Kwanaki bayan wasu kwanaki, Kiyosumi ya cigaba da yin hakan kullum na tsawon lokaci sosai. Har sai wata rana wasu yan mata suka zo suka bashi wani labari. Suka ce wasu daliban shekarar farko sun tare su bayan makaranta, suka hana su shiga ban daki sam ba zasu shiga ba. Kuma da alama akwai wasu a ciki suna yi wa wata daliba abu. Kiyosumi yana jin hakan, nan take yayi zargin dalibar da ake tura wa ita ce Hari. Ya tabbata Hari ce. Sai ya koma makarantar da gudu gwargwadon karfin sa. Daga nan ya nufi ban dakin yan mata kai tsaye domin ya tabbatar da zargin sa da kyau kyau sosai. A nan ya gano Hari tan kasa a wani lungu. Kiyosumi yayi sauri ya tambaye ta ya ce ta dauko mishi kin dake kasa. Amma Hari kawai tsayawa ta yi tana ta kallon sa.