Hook

Their other posts in the index, biggest breakout first.
So ina jin mamaki, mutum yana amfani da iPhone bai da application guda biyar da zan lissafa a wannan bidiyon. Application na farko shine Document Riddle. Da wannan application din zaka iya organizing kamar irin su file manager dinka, document da ake cewa ma da abubuwa da dama zaka iya yi da wannan Document Riddle din. Application na biyu shine CPU Dasher. Da wannan application din specifically wanda suke amfani da kamar irin iPhone 13 haka da irin su iPhone 13 Pro ma, iPhone 12 Pro ma wanda wayansu yake yi wani ta zafi, zaka iya amfani da wannan application din ka dan dinga cooling wayarka in yayi zafi. Kaga is a very important application da ya kamata ace kaje ka downloading. Sai kuma application na uku shine Battery Life. Da wannan application din zaka iya gani exact battery percentage na wayarka, ya battery percentage na wayarka yana sauka da wuri ko kuma baya sauka da wuri. A'a battery na wayarka yana da matsala ko bata da matsala, so zaka gani asalin percentage na battery na wayarka ba wannan kake gani a cikin settings na iPhone ba. Sai application na hudu shine Water Eject. Da wannan application din zaka iya, misali ace masu amfani da kananan iPhone din nan haka, wayarka ya fadi a cikin ruwa zaka iya amfani da wannan Water Eject din ka kunna wannan Water Eject din, so duk wani ruwa da ya shiga cikin wayar din, zai fito ma da shi. Sai application na biyar wato shine Remini. So me kuke jira? Ya kamata ku gaggauta zuwa ku downloading wannan application din. Ina tabbata in dai kai ma abokin amfani da iPhone ne, wannan application din zasu yi ma amfani da yawa sosai.